1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu Chauvin da laifin kisan kai

Abdul-raheem Hassan
April 21, 2021

Wata kotu a Amirka ta samu Derek Chauvin tsohon dan sandan kasar da laifin kashe bakar fata George Floyd da gangan, bayan danne wuyarsa har ya dena numfashi.

https://p.dw.com/p/3sJCC
Murder trial of former Minneapolis police officer Derek Chauvin
Hoto: via REUTERS

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da masu rajin kare bakar fata a Amirka, sun nuna jin dadi bayan da wata kotu a jihar Mennosota ta samu tsohon dan sandan kasar farar fata Derek Chauvin da aikata laifuka uku masu nasaba da kashe bakar fata George Floyd ba bisa ka'ida ba.

Jim kadan bayan shari'ar, an nuna 'yan sanda sun saka wa Chauvin ankwa a hannu sun wuce da shi kurkuku. "A yau na samu sukuni ta yadda zan iya barci. Na shafe kwanaki ina addu'a da fatan ganin wannan rana da za a hukunta Chauvin - cewar wani dan uwan marigayi George Floyd"

Kotun ba ta sanar da adadin shekarun da Chauvin zai shafe a gidan kaso ba tukuna, amma wasu na ganin mai yuwa ya yi shekaru 40. Sai dai masana shari'a na cewa yana da damar daukaka kara kan shari'ar indai yana da ja kan hukuncin.