1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Haramta wa jami'an kiwon lafiya shiga yajin aiki a Benin

Gazali Abdou Tasawa
June 29, 2018

Kotun tsarin mulkin kasar Benin ta ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na haramta wa ma'aikatan kiwon lafiya da na ma'aikatun shari'a da kuma jami'an tsaron shiga yajin aiki bai saba wa dokar tsarin mulkin kasar ba. 

https://p.dw.com/p/30Yka
Der Präsident von Benin Patrice Talon
Hoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Kotun tsarin mulkin kasar Benin ta ce matakin da gwamnatin kasar ta dauka na haramta wa ma'aikatan kiwon lafiya da na ma'aikatun shari'a da kuma jami'an tsaron kasar shiga yajin aiki bai saba wa dokokin tsarin mulkin kasar ba. Wannan hukunci da kotun tsarin mulkin kasar ta Benin ta bayyana a yammacin jiya Alhamis ya kawo karshen takun sakar da aka share watanni da dama ana yi tsakanin bangaren zartarwa da hukumar shari'a ta kasar wacce ta bayyana dokar haramcin yajin aiki da majalisar dokokin kasar ta sanya wa hannu a watan Janerun da ya gabata a matsayin wacce ta saba wa kundin tsarin mulkin kasar. A hukuncin da ta bayyana kan wannan batu dai kotun tsarin mulkin kasar ta Benin ta ce ya zamo dole ga jami'an tsaro da na kiwon lafiya da su gudanar da aikinsu ala kullin halin kuma ba su da izinin shiga yajin aiki kuma ba bu hujja daya da za iya dogaro da ita domin dakatar da aikin kiwon lafiya da na tsaro a kasar.