Kotu ta daure ′yar adawar Rwanda | Labarai | DW | 30.10.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta daure 'yar adawar Rwanda

Kotu ta daure Ingabire na tsawon shekaru takwas bisa cin amanan kasa da karyata kisan kare dangi na shekarar 1994.

Wata kotun kasar Rwanda ta daure jagorar 'yan adawar kasar Victoire Ingabire, na tsawon shekaru takwas, saboda cin amanan kasa da karyata kisan kare dangi na shekarar 1994.

Kotun ta kuma wanke Ingabire daga zargin nuna kabilanci da jawo rarrabuwar kai. Kotun ta ce, ta yi sassauci wajen yanke hukunci, saboda jagorar 'yan adawan ta rubuta wasikar neman sassauci ga shugaba Paul Kagame.

Tuni lauyan shugabar 'yan adawan na Rwanda Victoire Ingabire, ya ce za su daukaka karar wannan hukunci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar