1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta daure wanda ya yi lalata da karnuka a Ostireliya

August 8, 2024

Kotu a Ostireliya ta aike da wani bature dan kasar Burtaniya zaman kaso na shekaru 10 bisa samun sa da laifin yin lalata da karnuka da sauran wasu laifukka a arewacin Ostireliya.

https://p.dw.com/p/4jFK1
Hoto: Esther Linder/AAP/IMAGO

Kwararren mai kula da walwalar dabbobin Adam Britton ya amsa laifuka 63 masu nasaba da cin zalin dabbobi da kuma mallakar wasu kayayyakin lalata da kananan yara.

Rahotanni sun ce a tsakanin shekarun 2020 zuwa 2022, baturen ya sayo karnuka 42 da zummar kiwata su cikin yanayi na mutunci da mutuntawa amma kwatsam sai ya fara yi wa karnukan fyade tare da kashe wasu daga cikinsu sannan ya rika wallafa hotunan abubuwan da yake da yi da dabbobin a shafinsa na manhajar Telegram

Hukuncin da kotun Ostireliyan ta sanar a wannan Alhamis ya hana mutumin sake mallakar dabbobi har karshen rayuwarsa ko da kuwa bayan ya kammala zaman kasonsa na shekaru 10.