1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamerhe zai yi shekaru 20 na zaman gida yari

Abdourahamane Hassane
June 11, 2020

Kotu a Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 na zaman gida yari ga tsohon kakakin majalisar dokokin kasar Vital Kamerhe.

https://p.dw.com/p/3debA
Kongo Oppositionsführer Vital Kamerhe
Hoto: Imago/Belga/T. Roge

Kotun ta yanke masa hukunci ne bayan da ta sameshi da laifin yin sama da fadi da dukiyar kasar. Vtal Kamerhe darakta a fadar shugaban kasar na Kwango kana abokin kawancen shugaban na siyasa ana zarginsa da handame kudade kusan dalar miliyan 50 tare da hadin baki da wasu 'yan kasar Libanon. Kamerhe wanda ya yi takara a zaben shugaban kasa na Kwango a shekara ta 2018 ya janye takararsa a karshe domin goyon bayan takarar shuga Felix Tshisekedi wanda shi ma ya sha alwashin mara masa baya a zaben shekara ta 2023.