Kotu ta dakatar da sakin aure a Falasdinu | Labarai | DW | 28.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta dakatar da sakin aure a Falasdinu

Shugaban kotunan Musulunci na yankin Falasdinu Mahmoud Al-Habash, ya yi kira ga alkallan kotuna daban-daban da su dakatar da ayyana sakin aure a cikin wannan wata mai albarka na azumin Ramadana.

Palästina Gaza City Besuch Ai Weiwei (Getty Images/AFP/M. Abed)

Mata a yankin Gaza na Falesdinu

Cikin wata sanarwa da ya fitar, shugaban alkallan na Falasdinu ya ce ya dauki wannan mataki ne ta sabili da abubuwan da suka gani a shekarar da ta gabata, inda mutane suka yi ta sakin matayensu sannan daga bisani suka yi nadama.

A cikin wannan wata dai na Azumin Ramadan, wasu mutanen da ba su da abinci, ko kuma ba su samu sigarin da suka zuka ba, kan tayar da rikici a gidajensu, inda wani lokacin sukan daukan mataki na gaggawa na saki.