Kotu ta amince da dokar inshorar lafiya a Amirka | Labarai | DW | 25.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu ta amince da dokar inshorar lafiya a Amirka

Wannan doka da masu ra'ayin rikau ke kalubalanta ta tanadi bai wa marasa galihu damar samun garabasar tallafin kudin haraji a cikin jihohi 50 na kasar

Kotun Kolin kasar Amirka ta tabbatar da halalcin matakin gyaran fuska da Shugaba Obama ya yi wa dokar tsarin inshorar lafiyar al'umma ta kasar wacce masu ra'ayin rikau suka kalubalanta a gabanta.Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin shekaru ukku da kotun kolin kasar ta Amirka ke yin watsi da matakin kalubalantar wannan doka wacce ta tanadi fadada matakin inshorar lafiya ga talakkawa da sauran marasa galihu na kasar ta Amirka.

Tuni dai Shugaba Obama ya bayyana farin cikinsa da hukuncin kotun akan wannan doka wacce ya ce na ci gaba da kasancewa a tsaye duk da irin jerin kalubalan da ta ke fuskanta daga masu adawa da ita.Wannan hukunci da kotun ta bayyana na nufin cewa illahirin jihohi 50 na kasar ta Amirka za su ci gaba da samun garabasar tallafin kudaden haraji da shirin ya tanada.