Kotu a Najeriya na tuhumar Mustapha Umar | Labarai | DW | 02.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kotu a Najeriya na tuhumar Mustapha Umar

Babbar kotu da ke Abuja ta yanke hukuncin cewa mutumin da ake zargi da kai harin bom domin tarwatsa ofisoshin jaridun This Day da Moment yana da laifi.

Da ya ke yanke hukuncin mai shari'a Adeniyi Ademola ya bayyana cewa kotu ba ta gamsu da dalilan da wanda ake tuhuma ya gabatar ba, don haka ya zama wajibi ya fuskanci shari'a domin kare kansa.

Barrister Nurudeen Sulaiman shi ne lauyan da ke kare wanda ake tuhuma: Ya ce '' babu allaƙa tsakanin laifin da aka aikata da wanda ake tuhuma da aikata laifin, don haka daga shaidun da suke a gaban kotu da waɗanda ya bayar har da ma waɗanda suka ba da shaida muna da ƙwarin gwiwa ɗari bisa ɗari cewa mune za mu samu nasara a shari'ar.'' A ranar 26 ga watan Afrilun 2012 ne yan sanda suka cafke Mustapha Umar jim kaɗan bayan mumunan harin bom da aka kai a ofisoshin jaridar da ke Kaduna. A yanzu an tsayar da ranar 30 ga watan Satumba domin ci gaba da wannan shari'a da za a kai ga lokacin da za'a yanke hukunci.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar