1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu a Boston za ta fara yin shari'ar Djokhar Tsarnaev

Abdourahamane HassaneMarch 4, 2015

Nan gaba a yau wata kotu a birnin na Boston na Amirka za ta soma sauran ƙaran.

https://p.dw.com/p/1Ekvj
Djokhar TsarnaevHoto: picture-alliance/AP

Mutumin dai shi ka dai ya yi saura daga cikin waɗanda suka kai tagwayen hare-haren na ta'addanci a lokacin wata gasa ta gudun yada ƙanan wani a Boston.

A cikin watan Afrilu na shekara ta 2013 wanda a ciki mutane uku suka mutu yayin a wasu 264 suka jikkata.Tsarnaev mai shekaru 21 musulumin ne dan asilin ƙasar Kirghizstan kuma tun a can baya ya riga ya ammsa laifin kai harin. Ɗan uwansa dai Tamerlan wanda ake zargi da ba da haɗin kai an kasheshi a sa'ilin harin a cikin wata musanyar wuta da 'yan sanda.