Koriya ta Kudu: Moon Jae-In ya lashe zabe
May 9, 2017Talla
Rahotanni daga Koriya ta Kudu na cewa Moon Jae-In ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a wannan Talata a kasar bayan da ya samu kashi 41,1% na kuri'un da aka kada.
Koriya ta Kudu ta shirya wannan zaben gaba da wa'adi ne bayan da aka tsige tsohuwar shugabar kasar Park Geun Hye a sakamakon wata badakalar cin hanci da aka bankado a gwamnatin tata. Mutane sama da kashi 75% na wadanda suka cancanci zaben ne suka fito suka kada kuri'arsu inda da dayawa daga cikinsu suka yi amfani da wannan dama domin huce hushinsu kan 'yan siyasar kasar da suka yi kaurin suna wajen cin hanci.
Babban kalubalanen da ke a gaban sabon shugaban dai sune na matsalar tsadar rayuwa da rashin aikin yi da ake fama da su a kasar.