Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami | Labarai | DW | 09.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta yi nasarar sake jarraba harba wani makami mai linzami ta hanyar karkashin ruwan teku na gabashin yankin Asiya.

Ofishin ministan tsaro na Koriya ta Kudu wanda shi ya bayyana wannan labarin ya ce ana tsammanin cewar makamin da Koriya ta Arewan ta harba shi ne samfarin SLBM mai cin dogon zango. Daman a cikin watan Afrilun da ya gabata Koriya ta Arewan ta harba irin wannan makamin, wanda a lokacin jagoran mulkin kasar Kim Jong Un ya ce a yanzu suna da makamin da za su iya kai hari daga kasarsu har ya zuwa Koriya ta Kudu da kuma Amirka.

Wannan gwaji na makamin mai linzamin na Koriya ta Arewan ya zo ne a daidai lokacin da Amirka ta bai wa Koriya ta Kudu wasu rokoki masu kakkabo makamai masu linzami mafi inganci a duniya.