Koma bayan samar da makamashi a Afirka | Zamantakewa | DW | 24.03.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Koma bayan samar da makamashi a Afirka

Matsalolin cin hanci da rashawa gami da rashin iya tafiyar da harkokin gwamnati suna sake tabarbara tsarin samar da makamashi a nahiyar Afirka.

Kongo Staudamm Inga

Madatsar ruwa ta Inga da ke Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai na daga cikin kasashen, sai dai akwai wani katafaren tsari tun shekarun 1990 na bunkasa samar da makamashi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon a kogin da ake kira Inga, inda madatsar ruwan da ake ginawa mataki na daya da na biyu suka kai kimanin kilo-mita 150 cikin kogin mai nisan kilomita 4,700 kafin ya kwarara cikin Tekun Atlantika.

Tun shekara ta 2013 Afirka ta Kudu wadda take fama da matsalolin katsewar hasken wutar lantarki take shirye domin sayen adadi mai yawa daga wannan tsari. Tsarin yana da tasiri ga wagmnatin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, sai dai a shekara ta 2016 Bankin Duniya ya janye daga cikin kwantiragin saboda shugaban kasar na wannan lokaci Joseph Kabila ya mayar da aikin karkashinsa kai tsaye.

Duk da yanayin da ake ciki gwamnatin ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta samu masu zuba jari. Tun lokacin da gwamnatin Afirka ta Kudu karkashin Shugaba Cyril Ramaphosa ta dakatar da fadada tashohin nukiliya take neman hanyoyin da za ta kara yawan hasken wutar lantarkin daga kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya zama zabi na zahiri.