1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Koma bayan arziki na daukar hankali a taron Davos

Suleiman Babayo MAB
January 16, 2023

Shugabannin gwamnatoci da na manyan kamfanoni na duniya na halartar taron tattalin arziki na shekara-shekara a birnin Davos na kasar Switzerland. Matsalolin arziki da yakin Rasha da Ukraine ya haifar ne ke mamaye taron.

https://p.dw.com/p/4MFlS
Schweiz I WEF in Davos
Shugabannin da ke da ruwa da tsaki wajen shirya taron Davos na 2023Hoto: Laurent Gillieron/KEYSTONE/picture alliance

Daga cikin mahalarta taron, akwai kimanin shugabannin gwamnatocin kasashe 52 da manyan 'yan kasuwa 600 da suke jagorancin manyan kamfanoni na bangarori daban-daban na duniya. Yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine kimanin shekara guda da samun yawan masu kamuwa da annobar Covid-19 a Chaina da wasu rikice-rikice gami da sauyin yanayi, duk suna cikin abubuwan da za a tattaunawa a tsawon kwanakin da suke tafe lokacin taron na tattalin arziki na duniya a Davos.

Babbar daraktar kungiyar Oxfam ta duniya mai yaki da 'yunwa ta bayyana yadda rahotansu ke ci gaba da nuna irin gibin da ake samu tsakanin masu arziki da 'yan rabbana ka wadata mu.Gabriela Bucher ta ce" Kashi 1% na mutane na da kashi biyu bisa uku na dukiya da aka samu daga shekara ta 2020, abin da ya yi kusan nunka adadin abin da kashi 99 cikin 100 na al'umma suka mallaka. Haka lamarin yake tafiya cikin shekaru 10 da suka gabata, inda galibin sabbin dukiya ke ci gaba da kasance a hannun masu arziki 'yan tsiraru."

WWF Davos 2023 Auftakt, Gabriela Bucher, OXFAM
Gabriela Bucher, shugabar OXFAM ta jan hankali kan gibi tsakanin talakawa da attajiraiHoto: Fabrice Coffrini/AFP

Rahoton na kungiyar ta Oxfam ya kuma nuna cewa kamfanonin samar da abinci suna kara samun riba yayin da farashi ke ci gaba da tashi, inda kara haraji kan ribar da kamfanonin ke samu zai iya taimakawa wajen cike gibi tsakanin masu arziki da talakawa. Taron na Davos na zuwa lokacin da ake samun koma bayan tattalin arziki bisa matsaloli da dama suke karo da juna.

Schweiz I WEF in Davos I Borge Brende
Børge Brende ne shugaban taron tattalin arzikin duniya na birnin DavosHoto: Laurent Gillieron/KEYSTONE/picture alliance

Børge Brende da ke zama shugaban taron tattalin arzikin na duniya na cewa: "Akwai abubuwa da dama da suke jiran samun mafita na yake-yake da rikice-rikice. Sai mun samo mafita ga koma bayan tattalin arziki da shekaru 10 na tafiyar hawainiyar tattalin arziki wanda ba a gani ba tun shekarun 1970. Haka kuma masu ruwa da tsaki za su shiga hanyar samar da aiki mai inganci da za su taimaka ga bunkasan tattalin arziki na duniya."

Har yanzu duniya ba ta gama murmurewa daga matsalolin da annobar Covid-19 ta haifar ba, ga kuma yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine ya kara tabarbara lamuru, sannan tattalin arzikin duniya na gararamba. Sai dai duk da haka masu arziki suna kara arziki yayin da kamfanonin da suka mallaka suke kara samun riba.