Koma baya a yunkurin sulhunta rikicin Siriya | Labarai | DW | 27.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Koma baya a yunkurin sulhunta rikicin Siriya

Fatan sasanta rikicin kasar Siriya a taron da aka shirya yi a birnin Geneva ya fuskanci koma baya a sanadiyar sa-in-sa a bangarorin da ya kamata su halarci taron.

Batun tattaunawar ta wanzar da zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta ya fuskanci tarnaki biyo bayan bukatar ganin lallai sai shugaba Bashar al-Assad ya sauka daga karagar mulkin kasar, a yayin da gwamnatin Assad din ke ikirarin samun nasara a sake karbe ikon wasu yankunan kasar daga hannun 'yan tawaye.

A wani rahoto da wata jaridar kasar ta wallafa a wannan Litinin, ta ce wakilan gwamnati ba za su sami damar hallarta zaman sulhunta rikicin a gobe Talata kamar yadda aka tsara ba, sabili da matakin kungiyar hadaka da tace a fitar da shugaban daga lissafin kowacce gwamnatin rikon kwarya da za a kafa nan gaba in har an kai ga cimma yarjejeniya a taron na Geneva. Gwamnatin Siriya a na ta bangaren ta ce taron zai iya yin tasiri in har 'yan tawaye sun bi umarninta na  ajiye makamai. Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu tun barkewar yakin basasa a Siriya lamarin da aka ce ya haifar da matsalar 'yan gudun hijra mafi muni a tarihi.