1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a kan mulki a Venezuela

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
January 24, 2019

A kasar Venezuela jagoran adawa Juan Guaido ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, a wani sabon yunkuri na kifar da gwamnatin Shugaba Nicolas Maduro na kasar.

https://p.dw.com/p/3C6eJ
Venezuelas Parlamentschef fordert Präsident Maduro heraus
Hoto: picture-alliance/dpa/B. Vergara

A yayin da yake rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa na riko a Venezuelan, jagoran adawa kana shugaban majalisa Juan cewa ya yi: "Dalilin daukar wannan mataki shi na kawo karshen wannan gwamnati ta mulkin kama karya, tare da gudanar da sahihin zabe. In har hakan ta samu, al'ummar kasa za su bamu tukwici, idan kuma ba mu cimma nasara ba, sai su dauki matakin da ya dace."

Venezuela Juan Guaido Vereidigung Parlamentspräsident
Juan Guaido shugaban majalisar dokokin Venezuela da ya ayyana kana shugaban kasaHoto: picture-alliance/AP Photo/F. Llano

Tuni dai shugaban Amirka Donald Trump ya ayyana Guaido a matsayin halartaccen shugaban kasa a shafinsa na Twitter, yayin da kasashen kungiyar LIMA da ke kokarin ganin ta kawo karshen rikicin na Venezuela 13 daga cikin 14 suka nuna amincewarsu da matakin. Kasar Kanada na zaman guda daga cikin wadannan kasashe, kuma ta bakin ministar harkokin kasashen ketare ta kasar Chrystia Freeland ta nuna amincewarta da gwamnatin Guaido. A wata sanarwa da ta fitar Freeland cewa ta yi: "Bari in shaida muku cewa a madadin al'ummar Kanada, mun amince tare kuma da nuna cikakken goyon bayanmu ga gwamnatin rikon kwarya a Venezuela da shugaban majalisa Juan Guaido ya ayyana kafawa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Venezuela ya tanadar. Kana kungiyarmu ta Lima na shirin fitar da sanarwa na ba da jimawa ba. Wannan babbar rana ce ga al'ummar Venezuela."

A nasa bangaren, Shugaba Nicolas Maduro ya bayyana cewa Guaido da magoya bayansa na kokarin yi masa juyin mulki, inda ya bukaci sojojin kasar da su yi kokarin dawo da doka da oda. Sai dai tamkar sanya bakin Amirka ya fi yi wa Maduron zafi, domin kuwa ya dauki matakin yanke huldar diplomasiyya da Amirka, inda cikin dinbin magoya bayansa da ke sowa ya bai wa duk wasu jami'an diplomasiyyar Amirkan da ke kasar sa'o'i 72 su fice daga Venezuelan yana mai cewa: "Na yanke shawarar datse huldar diplomasiyya  da gwamnatin Amirka. Ku fice daga Venezuela, shisshigin ya isa, akwai mutumci a nan, al'umma za su kare kasarsu. A wannan rana mai dinbin tarihi ta samun 'yanci da sake tabbatar da cikakken iko, ina mai sanya hannu kan takardar yarjejeniyar diplomasiyya tare da bai wa jami'an diplomasiyyar Amirka sa'o'i 72 su fice daga kasarmu. Ina mai sanya hannu da sunan al'ummar Venezuela."

Nicolas Maduro
Nicolas Maduro shugaban da ake kokarin kwace wa mulkiHoto: picture-alliance/AP/A. Cubillos

Sai dai tuni sakataren harkokin kasashen waje na Amirka Mike Pompeo ya mayar wa da Maduro martani  a shafinsa na Twitter, yana mai cewa Amirka za ta ci gaba da yin huldar diplomasiyya da Venezuela a karkashin gwamnatin rikon kwarya ta Shugaba Juan Guaido.