1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: 'Yan adawa na son Ecowas ta sa bakinta a zabe

Salissou Boukari AMA
August 27, 2019

Kawancen jam'iyyun adawa na FRDDR da FP sun aike da wata wasika ga shugaban kwamitin gudanarwa kungiyar ECOWAS domin ganin ta saka bakinta kan rigingimun da ake fuskanta a gabanin zabe.

https://p.dw.com/p/3OVSU
Gangamin 'yan adawa kan shire-shiryen zabe a Nijar
Gangamin 'yan adawa kan shire-shiryen zabe a NijarHoto: Getty Images/AFP/B. Hama

Gamayyar jam’iyyun adawar na Jamhuriyar Nijar sun ce tura ta soma kai wa bango dangane da shirye-shiryen zabuka a Nijar, dalilan da ya sanya suka kai kokensu a gaban kwamitin gudanarwa na kungiyar ECOWAS domin duba lamarin da idon basira a wani mataki da rigakafin abubuwan da ka iya faruwa a kasar muddin ba a shirya tsarin zaben kasar kamar yadda kowa ya yarda da shi a Nijar ba.

'Yan adawar na zargin masu mulki da shirin amfani da kundin jerin sunayan masu zabe wajen yin abu da ake so, kana kuma ra'ayin jam’iyyun na adawa ya zo daidai da ake kiran da gamayyun jam'iyyun ‘yan baruwanmu suka yi ga ‘yan adawar na Nijar da su shigo cikin tsarin tafiyar da zabe maimakon kauracewar da suke yi  yau fiye da watanni.