Kokarin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. | Labarai | DW | 22.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amirka Donald Trump yace za'a sami zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya idan aka hada kai aka yi aiki tare.

Shugaban Amirka Donald Trump ya baiyana cewa zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya zai samu ne kawai ta hanyar hada hannu da kuma aiki tare.

Da yake jawabi jim kadan bayan saukarsa Israila a ranar litinin din nan a ziyararsa ta farko a yankin Trump yace babu wata hanya ta cimma masalaha face ta aiki tare.

Yace dama da ta samu a gare mu domin samar da tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki da jama'arta, Mu kawar da ta'addanci da samar da makoma ta wanzuwar lumana da zaman lafiya. Za mu iya cimma wannan mataki ne kawai idan muka hada hannu muka yi aiki tare.

Tun dai bayan da ya karbi ragamar mulki a watan janairu Trump yake nuna kwarin gwiwar cewa za'a cimma nasara, inda yake kokarin taimakawa Israila da Falasdinawa samun sulhun wanda yanzu ya faskara.