Kokarin warware rikicin Kongo | Labarai | DW | 21.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin warware rikicin Kongo

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci warware matsalolin da ke janyo cikas ga kokarin cimma daidaito a tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Kongo.

Jakadun majalisar Dinkin Duniya sun yi kashedi game da matakin da gwamnatin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da kuma 'yan tawayen kasar ke dauka na karfafa dakarunsu da ke yankin gabashin kasar, a dai dai lokacin da kokarin samar da zaman lafiya a tsakaninsu ya gamu da cikas. A dai wannan Litinin ce, masu shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya a tattaunawar sulhun da ke gudana a birnin Kampala na Uganda, suka dage taro a tsakanin gwamnati da 'yan tawayen M23.

Martin Kobler, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Kongo, ya ce akwai karin dakarun da gwamnati da ma 'yan tawayen suka kara adadinsu a birnin Goma da ke gabashin Kongo. Ita ma jakadiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa kasashen yankin manyan tafkuna, Mary Robinson, kokawa ne ta yi a kan karuwar dakarun, tana mai cewar hakan manuniya ce ga bukatar cimma yarjejeniyar sulhu a birnin Kampala. Ta ce tuni sassan biyu suka daidaita a kan batutuwa takwas daga cikin 12 na neman sulhu, inda sabani a kan shawarar yin afuwa ga 'yan tawayen M23 da kuma hanyar shigar dasu cikin rundunar gwamnati ya tilasta jinginar da tattaunawar.

Jakadun biyu dai sun bukaci sabunta kokari daga sassan da abin ya shafa, amma sun bayyana fargabar sake samun rarrabuwar kawuna a tsakanin mambobin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da zai gudanar da taro a kan matsalar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu