Kokarin warware rikicin kasar Masar | Labarai | DW | 29.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin warware rikicin kasar Masar

Bayan kissan dimbin magoya bayan tsohuwar gwamnatin Masar, Turai na shiga tsakani domin warware rikicin kasar.

Kantomar kula da manufofin ketare a kungiyar tarayyar Turai Catherine Ashton, ta isa Masar domin ganawa da hafsan sojin kasar da ya jagoranci kifar da gwamnati shugaba Mohammed Mursi a ranar ukku ga watan Yulin nan, wato, janar Abdel Fattah al-Sisi. Ashton, za ta kuma gana tare da jami'an jam'iyyar Freedom and Justice Party ta kungiyar 'yan uwa Musulmi, wadda sojojin suka kifar da gwamnatinsu.

A halin da ake ciki kuma, magoya bayan shugaba Mursi, na ci gaba da yin zaman dirshan, tare da neman sai an mayar da zababbiyar gwamnati, inda suka yi watsi da barazanar yin anfani da karfin da gwamnati ta yi alkawarin yi, da nufin kawar dasu a wurin da suke zaune, domin kuwa a cewarsu, suna boren lumana ne.

Rahotannin baya bayan nan da ke zuwa kuwa, na nuni da cewar, dubun dubatan magoya bayan Mursi ne ke yin dafifi zuwa hedikwatar hukumar leken asirin sojin da ke birnin alQahira, fadar gwamnatin kasar da sanyin safiyar nan.

Akalla magoya bayan Mursi 72 ne suka mutu sakamakon tsauraran matakan da sojoji suka dauka a kokarin kawar dasu daga wurin da suke zaman dirshen.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou