Kokarin neman sulhu a rikicin Siriya | Labarai | DW | 25.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin neman sulhu a rikicin Siriya

Za a sake komawa a kan tebrin tataunawa a yunkurin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a Siriya a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya a Vienna.

Wannan tattaunawa dai na zuwa a daidai lokacin da fada ke kara yin muni tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan tawayen a fagen dagga abin da ake gani zai iya yin kafar ungulu ga shawarwarin. Daman dai wata guda da ya wuce an gudanar da irin wannan taro a Geneve ba tare da samun daidaito ba tsakanin bangarorin biyu sakamakon yadda aka gaza yin tattaunwa ta gaba da gaba.