1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen rikicin Yukren

February 21, 2014

'Yan adawar kasar Yukren za su sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu da gwamnati amma sunce dolene a biya musu sauran bukatunsu.

https://p.dw.com/p/1BDOI
Hoto: Reuters

Jagoran adawar kasar ta Yukren Vitali Klitschko ne ya sanar da hakan, inda ya ce dolene kuma gwamnatin ta ci gaba da tattaunawa da 'yan adawar domin biya musu sauran bukatunsu. Wannan sanarwar ta 'yan adawar dai na zuwa ne bayan da Shugaba Viktor Yanukovych na Yukren din ya amince da wasu sauye-sauye a kasar sakamakon matsin lambar da ya ke fama da ita daga kasashen duniya kan ya kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar sa da ya haddsa asarar rayuka masu yawa.

Sauye-sauyen da shugaban na Yukren ya sanar da cewa za a gudanar a kasar sun hadar da yin gyara ga kundin tsarin mulki da gudanar da zabe a kasar nan bada jimawa ba tare kuma da daukar alkawarin sanya 'yan adawar a cikin gwamnati, sai dai kuma bai bayyana ko wanne lokaci ne za a gudanar da zabukan ba. Ministocin harkokin kasashen waje na kasashen kungiyar Tarayyar Turai dai sun kwashe tsahon daren jiya suna tattaunawa a Kiev babban birnin kasar ta Yukren da nufin tilastawa shugaba Yanukovych ya kawo karshen tashin hankalin da kasar tasa tsunduma ciki.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Zainab Mohammed Abubakar