Kokarin dakile yaduwar cutar Ebola | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Kokarin dakile yaduwar cutar Ebola

Baya ga kasar Guinea inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 60, an kuma samu labarin bullarta a kasashe makwabta irin su Liberiya da Saliyo.

Labarin bullar cutar Ebola a wasu kasashen yammacin Afirka ya fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan makon. A labarinta mai taken “An hana cin naman jemage” jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi.

„Don dakile yaduwar kwayoyin cutar Ebola gwamnatin kasar Guinea da ke yammacin Afirka ta dauki wani mataki da ba a saba gani ba. Kwanaki biyu a jere ministan kiwon lafiya Rene Lama ya yi balaguro a wasu yankunan kasar da ke kan iyaka da kasar Liberiya, yankin kuma da ake kyautata cewa nan ne cibiyar kwayoyin cutar. A duk wuraren da ya gana da jama'a sai ya cire mataccen jemage daga jakarsa ya nuna wa jama'a yana cewa, kun ga wannan to ku nesanci cinsa. An dai hakikance cewa jemage ne ke yada kwayoyin cutar ta Ebola, ko da yake bincike ya nuna cewa a matakin farko cutar na yaduwa ne idan aka ci naman biri da ke dauke da kwayoyin cutar. Baya ga kasar Guinea inda cutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 60, an kuma samu labarin bullarta a kasashe makwabta irin su Liberiya da Saliyo. Su kuma a na su bangaren likitocin kungiyar agaji ta Medicins Sans Frontier sun kafa wasu kebabbun cibiyoyin ba da magani guda biyu a yankunan da abin ya fi muni.“

Rikici a Afirka ta Tsakiya shekara guda bayan juyin mulki

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel ta leka Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne mai fama da tashe-tashen hankula, inda a farkon wannan mako aka cika shekara guda da yin juyin mulki.

Anti-Balaka Kämpfer Bangui

Mayakin Anti-Balaka a Bangui

„Shekara guda daidai da juyin mulki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta gaggauta tura karin sojoji zuwa wannan kasa. Duk da cewa akwai tawagogin wanzar da zaman lafiya, amma har yanzu Kwamitin Sulhu ya kasa hada kansu karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya. Ita ma shugabar wucin gadi Catherine Samba-Panza wadda tun a cikin watan Janeru take jagorantar gwamnatin rikon kwarya a birnin Bangui, ta yi wannan roko sau da dama. Amma har yanzu wadannan kiraye-kiraye ba su haifar da abin da ake bukata ba. Har yanzu dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka Misca da tawagar Turai Eufor da dakarun kundunbala na Faransa wato Sanagri sun kasa kawo karshen kashe-kashen da ake yi musamman wanda ‚yan bangar kungiyar Anti-Balaka ke yi.“

Aiwatar da manufofin Jamus game da Afirka

Frank-Walter Steinmeier auf Afrika-Reise Äthiopien

Steinmeier a Habasha

Fata na gari lamiri inji jaridar Süddeutsche Zeitung tana mai tsokaci ga rangadin kasashen Afirka uku da ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya yi a wannan mako.

„Bayan ziyarar da ministan ya kai nahiyar ta Afirka abin da ake bukata yanzu shi ne a gani a kasa wato aiwatar da sabbin manufofin Jamus ga nahiya. Kamata ya yi dukkan ma'aikatu daban-daban na gwamnatin Jamus su karfafa hadin kan aikace-aikacensu ga wannan nahiya. Afirka dai nahiya ce da a daya bangaren ake fama da tashe-tashen hankula, amma kuma a bangare daya ana samun bunkasar tattalin arziki cikin sauri a wasu kasashenta. A mako mai zuwa za a gudanar da wani taron koli tsakanin kungiyar EU da Afirka a birnin Brussels, taron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke cikin wadanda za su halarta.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe