Kofin nahiyar Afirka: Fitattun 'yan wasa
A wasan kasashen Afirka a Gabon hankali ya koma kan Cote d’ivoire da ke neman rike kambunta sai dai akwai kasashe da dama da suka kawo gaci da ‘yan wasansu: Ga wasu taurari:
Boyayyun 'yan wasa na son baje bajintarsu
A kiyasin hukumar FIFA ana bayyanasu cikin manya a tawagar ‘yan wasan Afirka, duk da rasa samun dama ta zuwa wasan kwallon duniya tun a shekarar 2002, Senegal na neman samun nasara. A kulob din Liverpool Sadio Mane (hagu) ya kasance daya cikin zakarun ‘yan wasa a Afirka.
Giwa gagara badau
A shekarar 2015 sun zama zakarun wasan da yanzu ido ya karkata kansu, an yi "shahararrun 'yan wasa" Didier Drogba da Yaya Tourè a wannan kasa, duk da haka mai horas da ‘yan wasa Michel Dussuyer na da wasu kwararrun wadanda suka taka leda a Premier League kamar Wilfried Bony (a gaba) da Wilfried Zaha da Eric Bailly.
Gwani na gwanayen masu karbar baki
Duk da cewa ba su taka wata rawar a zo a gani ba a wasanni takwas da suka gabata, masu masaukin baki, fatansu ya dogara ga gwanin dan wasa a kulob din Borussia Dortmund Pierre-Emerick Aubameyang (hagu) dan wasan da a bana a farkon kakar wasa ya zama dodon raga.
Ko Mahrez zai sake daga wani kambun?
Daya daga cikin masu cimma nasara a boye Aljeriya, ta yi nasara zuwa wasan kwallon duniya sau biyu a baya, inda a shekarar 2014 sai da aka kara lokaci bayan cikar lokacin wasansu da Jamus, sai dai duk da nasara a duniya tawagar ta Desert Foxes a wasan na AFCON rabansu da nasara tun a shekarar 1990. Dan wasansu Riyad Mahrez (hagu) zakaran kwallon kafar Afirka na bana na zama abin dogaro.
Black Stars na son wani matsayi a bana
Bisa al’ada sun kasance a bangaren kulob masu karfi a Afirka, yanzu ba su da ’yan wasa gwanaye kamar a da amma dan wasan West Ham Andre Ayew (dama) ya kasance dan wasa mai hadari. Ghana dai ta ci wannan kofi sau hudu a baya. Abin takaici a shekarar 2015 an fitar da su a wasansu da Cote d’ivoire da ke zama na karshe a bugun da kai sai mai tsaron gida.
Dawowar tsofaffin masu sarauta
Bayan da suka gaza nasara ta samun zuwa gasar ta nahiyar Afirka sau uku, gasar da suka daga kofinta sau bakwai a baya, a wannan karo sun dawo da yunwar samun nasara a shekarar 2017. Mohamed Salah (tsakiya) na zama dan wasa da ke zama barazana ta kai hari yayin da Mohammed Elneny ke mara masa baya.
Kwarewar masu horas da 'yan wasa
Moroko ta kasance da fari ita za ta dauki bakuncin wasan a shekarar 2015 sai dai an aje ta gefe bayan da ta nemi a dage wasan saboda bullar cutar Ebola a Yammacin Afirka, Equtorial Guinea ta shigo ta karbi wasan. Yanzu Aziz Bouhaddouz (hagu) da takwarorinsa na son nuna irin bajintarsu. Mai horas da su Herve Renard ya san aikinsa, ya kai Coted’ivoire ga daga kofi a shekarar 2015.