Ko shugaba Akufo ya cike alkawura a Ghana? | Siyasa | DW | 07.12.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ko shugaba Akufo ya cike alkawura a Ghana?

Shekara guda da ta wuce, da yawa daga cikin al'ummar Ghana suka yi bikin nasarar da daddaden madugun adawar kasar Nana Akufo-Addo ya samu a zaben shugaban kasa a ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2016.

An samu wannan sauyi cikin kwanciyar hankali da lumana ba da wata hatsaniya ba, masana'anta daya a kowace gunduma, ba da ilimin sakandare kyauta, karin zuba jari daga ketare da yaki da cin hanci da rashawa. Wadannan na daga cikin alkawuran da Nana Akufo-Addo ya yi a bara lokacin da ya sake tsayawa takarar neman shugabancin kasar Ghana, kuma ya yi nasara a kan shugaban da ke kan karagar mulki John Dramani Mahama.

Duniya ta gamsu da nasarar samun sauyin mulkin karo na hudu cikin lumana a kasar ta Ghana, da yawa daga cikin al'ummar kasar kuma sun yi fatan bude wani sahihin sabon babi. Sabon shugaban kasar ya kwashe kusan rabin shekara kafin ya kammala hada kan majalisar ministocinsa. Tun sannan ne kuma gwamnati ta fara nazari kan jerin alkawuran da ta dauka.

Afrika Ghana - Unterstützer feiern Nana Akufo-Addo der die Präsidentschaftswahl gewann (picture-alliance/AP Photo/Sunday Alamba)

Mata na murnar nasarar shugaban kasar Nana Akufo-Addo

A cikin watan Satumba ta fara aiwatar da shirin ba da ilimin sakandare kyauta a makarantun gwamnati. Ta ce shirye-shirye kuma sun yi nisa na gina madatsun ruwa da masana'antu a dukkan gundumonin kasar. Sai dai ba a cika alkawarin hukunta jami'an da aka same su da laifin cin hanci da rashawa, duk da cewa an kirkiro da wata hukuma ta musamman da nufin yakar cin hanci da rashawa.

Kwame Danso Acheampong mai sharhi ne a fannin siyasa da ya ke ganin yadda 'yan Ghana suka damu, ya zama wajibi shugaba Nana Akufo-Addo ya yi hobasa a cikin watanni masu zuwa, ya ce:

"Idan ka dubi yadda abubuwa ke gudana, yaki da cin hanci da rashawa daya ne daga cikin muhimman batutuwan da shugaban ya yi wa 'yan kasa alkawari. Amma idan ka dubi take-taken yaki da cin hanci, za ka ga cewa yawanci sun kasance fatar baka ne kawai."

Ghana Präsidentschaftswahlen Nana Akufo-Addo Mitte-Links (Getty Images/AFP/C. Aldehuela)

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo tare da magoya bayansa

Sai dai Burkhardt Hellemann na gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus da ke Accra babban birnin kasar, ya ce bai yi mamakin yadda gwamnatin Ghanar ke tafiyar hawainiya wajen aiwatar da alkawuran da ta dauka ba, ya ce:

"A gani na cikin kwazo da kyakkyawan fata wannan gwamnati ta fara aiki, amma yanzu ta gane cewa bayan shekaru takwas tana bangaren adawa, tafiyar da gwamnati ba a bu ne mai sauki kamar da ta yi tsammani da farko ba."

Hellemann ya kara da cewa ko da yake matakin gaggawa na kawo sauyi a harkar ba da ilimi da gwamnati dauka ya samu karbuwa a wajen 'yan kasar, amma akwai aiki a gaba musamman wajen dorewar shirin ba da ilimin kyauta, ganin yadda gwamnati ta gaji basassuka daga tsohuwar gwamnati. Wani batun kuma shi ne na samar da aiki ga matasa, inji Hellemann na gidauniyar Konrad-Adenauer, ya ce: "Al'umar kasar suna son an kirkiro da guraben aiki. Sai dai ba za a iya magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa a ckin shekaru biyu ko uku ba, ko da kuwa an kafa sabbin masana'antu ne, domin za su dauki tsawon lokaci kafin sun zauna da gindinsu."

Gwamnatin ta Ghana dai ta dukufa wajen shawo kan kamfanoni da 'yan kasuwa na ketare da su zuba jari a kasar.