1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mahara sun hallaka fararen hula 38 a kasar Mali

Abdoulaye Mamane Amadou
June 19, 2019

Wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari a wasu garuruwa biyu da ke yankin tsakiyar kasar Mali tare da hallaka fararen hula 38 da kuma jikkata wasu da dama.

https://p.dw.com/p/3KgQs
Mali Angriff auf das Dogon-Dorf Sobane Da
Hoton wani harin da aka kai a kauyen 'yan kabilar Dogon a ranar 11 ga watan YuniHoto: Reuters/M. Konate

Akalla mutane 38 ne suka hallaka a wani harin da wasu masu dauke da makamai suka kai wa wasu garuruwa biyu na 'yan kabilar Dogon da ke kasar Mali kusa da iyakar kasar da Burkina Faso.

Gwamnatin kasar ta Mali ta tabbatar da faruwar labarin a kauyukan Gangafani da Yoro, tare da bayyana cewar tana daukar matakin tsaro ta hanyar tura karin jami'an tsaro inda tuni suka soma sintiri a yankin, sai dai babban alkalin alkalan kasar da ke jagorantar wata cibiyar da ke yaki da ta'adanci ya ce adadin mutanen da suka mutu 14 ne kawai.

Ko a ranar tara ga watannan watan na Yuni wasu masu dauke da makamai sun kai farmaki a wani kauyen na 'yan kabilar Dogon tare da hallaka mutane 35 galibinsu mata da kanana yara.