Kisan direban Tasi a Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 25.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kisan direban Tasi a Afirka ta Kudu

Wata kotu a Afirka ta Kudu ta samu wasu tsofaffin jami'an 'yan sandan kasar takwas da laifin kisan wani direban Tasi dan kasar Muzambik.

Samun wasu 'yan sanda a Afirka ta Kudu da laifin kisa

Samun wasu 'yan sanda a Afirka ta Kudu da laifin kisa

Rahotanni sun nunar da cewa 'yan sandan sun kama direban Tasin mai suna Mido Macia bayan da ya ajiye motarasa ba bisa ka'ida ba, inda suka lakada masa duka kana suka daure shi a jikin motarsu suka kuma ja shi a kan titi a wata hanya mai yawan jama'a da ke yankin Daveyton na birnin Johannesburg. Daga bisani ran Macia ya yi halinsa a yayin da yake tsare a hannun 'yan sandan sakamkon buguwa da ya yi a kansa yayin da suke jansa da motar. Tun dai a shekara ta 2013 da abin ya faru rundunar 'yan sandan kasar ta kori baki dayan jami'an takwas da ma kwamandan da suke karkashin kulawarsa. Wani wanda ba a bayyana sunansa ba cikin mutanen da lamarin ya afku a gabansu ne ya dauki yadda 'yan sandan suka ci zarafin mamacin a faifayen vedio tare da yada wa.