1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiran garambawul ga kwamitin sulhu

September 21, 2005

Jawabin Scharith, karamin minista a ma'aikatar harkokin wajen Jamus ga babbar mashawartar MDD

https://p.dw.com/p/BvZU
Klaus Scharioth
Klaus SchariothHoto: AP

A cikin jawabin nasa Klaus Schrioth, karamin minista a ma’aikatar harkokin wajen Jamus yayi bayani filla-filla a game da matsayin Jamus dangane da MDD da kuma shawarwarin da take ganin sun dace a game da canje-canjen da za a yi wa majalisar. Jami’in siyasar, wanda ake rade-radin cewar, mai yiwuwa a nada shi jakadan Jamus a birnin Washington nan gaba, yayi kira ga mahalarta zauren babbar mashawartar MDDr da su yi wa Allah da Ma’aiki su sa ido wajen ganin lalle an cika alkawururrukan da aka yi a taron kolin da shuagabannin kasashen majalisar suka gudanar makon da ya wuce domin cimma manufofin da aka zayyana na raya makomar kasashe masu tasowa nan da shekara ta 2015. Kazalika yayi bayani filla-filla a game da ire-iren nauyayan ayyuka da MDD ke gabatarwa a cikin shekaru da watannin baya-bayan nan a sassa daban-daban na duniya. Schariot ya ce wannan wata shaida ce game da kokarin majalisar na ba da kariya da taimako da tabbatar da zaman lafiya da kuma ayyukan sake ginawa, inda ya ce babban misali a nan shi ne kasar Afghanistan, wadda ya ce har kwanan gobe Jamus zata ci gaba ba ta goyan baya. A lokacin da ya waiwaya zuwa Iraki, jami’in siyasar ya gabatar da alkaluma dalla-dalla dangane da gudummawar da Jamus ke bayarwa ta fannin kudi da shawarwari domin dora kasar akan wata madaidaiciyar hanya ta demokradiyya da aikin doka da oda.

Babban burinmu shi ne gannin dukkan al’umar kasar Iraki sun fita daga cikin hali na zaman dardar da kuma mummunar wahalar da suke fama da ita yanzu haka. Bai kamata a saduda ga matakai na ta’adda da ta da zaune tsaye da ke neman zama gagara-badau a wannan kasa ba. Yankin gabas ta tsakiya na bukatar wata kasa ta Iraki dake da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma bunkasa akan manufa.

Har yau dai ana cikin hali na damuwa a game da shirin nukiliya na kasar Iran, inda aka yi wa lamarin rikon sakainar kashi ta yadda aka wayi gari murna na neman komawa ciki dangani da ci gaban da aka samu kwanan baya, in ji Schariot, mai jibintar ministan harkokin waje Joschka Fischer a taron babbar mashawartar MDD a birnin New York. Jami’in yayi amfani da wannan dama domin yin hannunka mai sanda ga kasar Amurka dangane da take-takenta game da matsalar, inda yake cewar:

Idan muna fatan hana yaduwar muggan makamai na kare-dangi, to kuwa wajibi ne kowace kasa ta rungumi alkakin da ya rataya wuyanta da hannu biyu-biyu. Kuma a lokaci guda wajibi ne a gabatar da nagartattun matakai domin ba wa manufar kwance damarar muggan makamai sabon jini.

Schriot ya kara da yin kira ga dukkan kasashen MDD da su sa baki wajen ganin an yi wa manufofinta garambawul, kama daga manufar kafa wata hukuma mai kula da manufofin zaman lafiya zuwa ga kirkiro wata sabuwar majalisar kula da manufofin girmama hakkin dan-Adam da kuma kwaskwarima ga tsarin kwamitin sulhu. Har yau dai Jamus da kawayenta na Brazil da Indiya da Japan suna kan shawararsu ta garambawul, in ji shi.