Kiran da paparoma ya yi a bikin Ista | Labarai | DW | 31.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiran da paparoma ya yi a bikin Ista

Paparoma Francis ya jagoranci bikin ista a karon farko tun bayan da ya dare kan wannan mukami inda ya nemi a warware rigingimu da ake fama da su a duniya cikin ruwan sanyi.

Shugaban Kiristoci mabiya dakikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya jagoranci dubban mabiya a dandalin St Peters da ke fadar Vatican wajen shagulgular bikin ista da ke zama daya daga cikin bukukuwa mafiya daraja ga Kiristoci.

Cikin jawabinsa Paparoman ya nemi ganin an sasanta cikin ruwan sanyi tsakanin kasashen Koriya, tare da fatar ganin bayan rikice-rikice da ake samu a kasashe kamar Najeriya da Siriya da Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ma dai Iraki da sauran wurare.

A rana irin wannan a ka hakikance Yesu Almasihu ya tashi daga matattu. Tun ranar Jumma'a a ka fara wadannan bukukuwa na isata wadanda ake kammala zuwa gobe Litinin.Wannan ya zama karo na farko da Paparoma Francis, dan kasar Argentina ke jagorantar bukukuwan, bayan zaben da a ka yi masa ranar 13 ga wannan wata na Maris.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe