Kiran ƙasashen larabawa ga Hamas | Labarai | DW | 16.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiran ƙasashen larabawa ga Hamas

ƙasashen larabawa sun buƙaci Hukumar gudanarwar Palasɗinawa ƙarƙashin jagorancin Hamas, ta amince da shawarar zaman lafiya da Israila bisa yarjejeniyar 1967. sai dai ministan harkokin wajen Palasɗinawa Mahmoud al-Zahar, wanda ke ziyarar ƙasashen larabawa domin neman taimakon kuɗi na gaggawa yaƙi cewa komai a game da buƙatar wadda ta saɓa da ƙudirin Hamas na ƙasa ɗaya ta islama a yankin Palasɗinawa. Mahmoud Zahar ya shaidawa manema labarai cewa ya yi Imani gwamnatocin ƙasashen larabawa za su taimakawa gwamnatin Hamas da gudunmawar kuɗaɗe bayan da ƙungiyar tarayyar turai, ta janye bata tallafi, saboda ƙin amincewar Hamas da wanzuwar ƙasar Israila. Zahar ya kuma gana da sakataren ƙungiyar ƙasashen larabawa Amr Moussa, inda suka tattauna a game da shawarwarin sulhu da aka gabatarwa Israila a shekara ta 2002 waɗanda Israila ta yi fatali da su. A waje guda kuma gwamnatin ƙasar Rasha, ta yi alkawarin baiwa Hamas tallafin gaggawa. A wata hira da suka yi ta wayar tarho ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov ya shaidawa shugaban hukumar gudanarwar Palasɗinawa Mahmoud Abbas, cewa Rasha, a shirye ta ke domin taimakawa Hamas da gudunmawar agaji. Mahmoud Abbas ya baiyana gamsuwa da karimcin da Rashan ta nuna na tallafa musu. A makon da ya gabata, Rasha, ta soki lamirin ƙasashen yammacin turai na janye tallafin kudin da suke baiwa gwamnatin Palasɗinawa.