Kira kan magance matsalar kasar Libiya | Labarai | DW | 19.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kira kan magance matsalar kasar Libiya

Wakillan kasashe 11 na Afirka sun hallara a wani babban zama a birnin Nouakchott, a kasar Mauritaniya, inda suka yi kira ga kasashen duniya da sun ceto kasar Libiya.

A cewar Kwamishinan Tarayyar Afirka a fannin zaman lafiya da tsaro Smaïl Chergui, kama daga Tarayyar Afirka, da kuma wannan mataki na birnin Nouakchott, ya kyautu kowa ya ba da himma na ganin an taimaka wa dangi 'yan kasar Libiya fita daga mawuyacin halin da suka shiga na rishin tsaro tun bayan kifar da gwamnatin marigayi Muhammar Khadafi a shekara ta 2011.

Shugaban kasar ta Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz kuma shugaban kungiyar Tarayyar Afirka yayin wani taron manema labarai cewa ya yi, suna fatan ganin tattaunawar da ake yi da masu shiga tsakani a rikicin kasar ta Libiya ta kai ga samun mafita.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu