Kira ga taka tsan-tsan ga ′yan gudun hijirar jihar Adamawa | Siyasa | DW | 23.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kira ga taka tsan-tsan ga 'yan gudun hijirar jihar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa dake Arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya, ta gargadi masu saurin komawa garuruwan da aka kwace a hannun Boko Haram da suka dakata don Gudun fadawa cikin hadaruruka.

A kokarinta na ganin ta kare lafiya da mutuncin Al'ummarta daga fadawa cikin masu ayyukan sari ka noke na 'yan kungiyar Boko Haram da ake cimma nasaran fitar dasu daga yankunan Arewacin jihar Adamawa, gwamnatin jihar ta gargadi masu marmarin komawa garuruwansu da su dakata har ya zuwa wani lokaci. Kwamishinan yada labarai na jihar Abdurahman Prambe, ya yi kira ga al'ummar Michika da su jinkirta komawan har sai gwamanti ta sanar da hakan a hukumance.

"Ya ce kafin a baiwa al'umma damar komawa akwai wasu matakai, domin kuwa sai jami'an tsaro sun tabbatar da ko ina na lafiya, ta yadda mutane zasu samu damar zama ba tareda matsala ko fargabar rayuwarsu ba. To amma idan ba sojojin sun baiyana hakanba akwai matsala ko da kuwa sun koma, ba zasu samu kwanciyar hankaliba...."

Mutane da dama dai sun bayyana ra'ayoyinsu kan wannan batu, inda suke ganin cewa lalle ya kyautu su yi taka tsan-tsan kan batun komawa ga gidajan nasu cikin sauri duk kuwa da cewa tuni hankalin wasu ya karkata ga komawa gidajen nasu na asali.To sai dai kuma garuruwan da gwamnatin ta jiha ta umarci al'umma su koma a hukumance ma kamar su Mubi, ana fuskantar dumbun matsaloli kamar na tsadar rayuwa.

Sauti da bidiyo akan labarin