1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga amfani da dadadan kalamai tsakanin shugabannin addini a Najeriya

January 25, 2013

kungiya tabbatar da zaman lafiya a Najeriya ta nemi shugabannin addinai da su guji yin amfani da kalaman batanci a wuraren ibada idan su na so a kawar da rarrabuwar kawuna.

https://p.dw.com/p/17RmI
Hoto: dapd

A karan farko kungiyar tabbatar da zaman lafiya da sasantawa tsakanin musulmi da kirista ta kira wani taron manema labarai a Kaduna da zumar janyo hankalin daukacin shugabannin addinai da na gargajiya a cikin kasar, domin nazarin hanyoyin gujewa amfani da kalaman da basu cancanta. Makasudin wanan taron dai shi ne neman magance matsalar da ke haifar da rigingimun addinai da na kabilanci tare ma da na siyasa. Ana danganta su da kaucewa karantarwar Alqur'ani da kuma Injila da ke horo da zama lafiya.

Matsayin shugabannin addini da kungiyoyin Najeriya

Shugaban kungiyar Peace Revival and Reconciliation Movement a Najeriya Pastor Yohanna Buru  shi ne ya shirya wannan taron. Yayi amfani da wannan  dama wajen nunar da cewa Najeriya za ta farfado da martabar da aka santa da ita a baya, da zarar shugabannin addinai suka taka rawar da ya kamata ta hanyar gudanar da wa'a'zi, da kuma yin watsi da haramtattun dabi'u da basu dace ba ga jagororin addinai ba.

Christliche Kirche und im Hintergrund Moschee in Abuja, Nigeria
Hoto: Katrin Gänsler

Kungiyoyin kare hakkin bil Adama da masu fafatukar ci-gaban al'umma sun dade suna kokawa dangane da irin rawar da malaman ke takawa a harkokin siyasar kasar wajen tursasa jama'a zaben shuwagabanin da basu cancanta ba. Sheikh Mohammed Nasiru Musa, wani malamin addinin musulunci ne a Nigeria dake ganin cewa kamata ne ya yi malaman addinai su yi wa'azin wanzar da zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankalin bayin Allah, ba wai su zamo masu taya gwamnati zaben gurbatattun shugabannin ba.

Burin da aka sa a gaba a taron na Kaduna

Mahalarta wannan taro dai da suka fito daga wurare daban daban sun tofa albarkacin bakin su. Malam Abdulrahman Mohammed shima dai wani babban malamin addini musulunci a kaduna dake cewa akwai wasu 'yan siyasa da ke amfani da malamai wajen tayar da zaune tsaye.Pastor Maxwel Sanda daga babban cocin Christ Evengelican a kudancin kaduna kira ne yayi ga malamai da sun koma ga kiran litattafan guda biyu.

NO FLASH Moschee Nigeria - Abuja
Hoto: picture-alliance/dpa

Burin da kungiyoyin wanzar da zaman lafiya a Najeriya ta sa samun dauwamanmiyar zaman lafiya tsakanin mabiya addinan guda biyu wato musulunci da kuma kiristanci. Kazalika ta na yin gargadi ga malamai kan illar furta kalaman batanci, ko na tursasawa jama'a a lokutan zabe.

Mawallafi: Ibrahima Yakubu
Edita: Mouhamadou Awal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani