Kinjeketile Ngwale: Madugun bore Maji-Maji | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 04.04.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Kinjeketile Ngwale: Madugun bore Maji-Maji

Kinjeketile Ngwale ginshiki na yakar Turawan mulkin mallaka na kasar Jamus a Tanganyika wanda yanzu ake kira Tanzaniya. A farkon karni na 20 ya zaburar da mutanen Tanganyika wajen bijire wa Turawan mulkin mallaka.

Inda ya rayu:

Yankin Ngarambe da Matumbi a Tanganyika wanda yanzu ake kira Tanzaniya. Turawan Jamus sun rataye shi a watan Agustan 1905 saboda samunsa da laifi na cin amanar kasa.

 

Shahara:

·  Shi ne mamallakin aljanin nan mai suna Hongo wanda aka ce ya fito a siffar maciji kana ya shigar da Kinjeketile cikin teku kuma da ya fito bayan sa'o'i 24 kayansa sun kasance ne a bushe. A wannan lokacin ne Kinjeketile ya fara fadin irin abubuwan da za su faru a gaba.

·  Hade kan kabilu dabam-dabam wanda ake ganin ita ce danba ta farko ta sanya kishin kasa a zukatan 'yan Tanganyika.

·  Ya yi wa magoya bayansa alkawari cewar harsashin Jamusawa ba zai tabasu ba in har suka yi amfani da ruwan maganinsa na Maji.

·  Shi ne ya assasa bore nan na Maji-Maji ko da dai ya rasu jim kadan bayan da aka fara boren. An yi yakin na Maji-Maji ne tsakanin 1905 zuwa 1907 kuma shi ne bore mafi girma da aka taba yi wa Turawan mulkin mallaka a Afirka.

A dubi bidiyo 01:49

Kinjeketile Ngwale: Madugun bore Maji-Maji

Sukar da aka rika masa: 

Jawowa mutane halaka sakamakon gaya musu da ya yi cewar maganin Maji zai basu kariya daga harbin bindiga. Bisa kiyasi kimanin mutane dubu 180 zuwa dubu 300 ne suka rasu lokacin boren Maji-Maji sakamakon rikicin da aka yi da kuma ja'ibar yunwa. Wannan mace-mace da aka samu dai ya rage yawan al'ummar kasar da kashi daya cikin uku.

 

Abin koyi: 

A shekarar 1969 shaharren marubucin nan Ebrahim Hussein ya fidda wani wasan kwaikwayo mai suna "Kinjeketile” wanda aka gina shi a kan Kinjeketile da kuma yakin Maji-Maji.

 

Karkashin shirin na musamman da DW kan tsara na Tushen Afirka bisa tallafi na gidauniyar Gerda Henkel.

Sauti da bidiyo akan labarin