Kimanin yara mata miliyan bakwai ke haihuwa a shekara | NRS-Import | DW | 30.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

Kimanin yara mata miliyan bakwai ke haihuwa a shekara

Hukumar kula da yawan jama'a ta duniya ta ce ta damu matuka saboda yawan 'yan matan 'yan kasa da shekaru15 da kan samu juna biyu wanda hakan kan yi illa ga lafiyarsu.

A cikin wani rahoto da ta wallafa, hukumar kula da yawan al'umma ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya ta galibin wannan matsala ta yawaita kananan yara masu juna biyu na samuwa a kasashe masu tasowa.

Werner Haug guda ne dagcikin daraktocin hukumar ya ce "yara mata kimanin miliyan bakwai da dubu dari uku ne ke samun juna biyu a kowacce shekara, kuma miliyan biyu daga cikin wannan adadin 'yan kasa da shekaru sha biyar ne. Yanayin girmansu da ma hankalinsu bai kai a ce sun zama iyaye ba."

Daga cikin wannan adadi da rahoton ya ce ana samu a kowacce shekara, 'yan shekaru sha hudun da aka ce sun kai miliyan biyu sun fi fuskantar matsaloli sama da saura. Wani batu da rahoton ya haska shi ne yanayin da yaran ke haihuwa duba da girmansu da yawan shekarunsu kamar dai yadda Werner Haug ya yi tsokaci.

"Galibin irin wannan haihuwar da ake samu, ana yinta ne ta hanyar yi wa matan da ke dauke da juna biyu tiyata maimakon su haihu da kansu. In aka yi rashin sa'a babu kyakkyawan tsari na kiwon lafiya to a kan ci karo da matsaloli wanda kan kai ga jawo rasa ran mai jegon ko na abin da ta ke dauke da shi."

Rahoton dai ya danganta wannan matsala da ake samu da talauci da kuma rashin ilimi da ma dai sauran matsalolin da kasashe masu tasowa ke fuskanta na rashin cigaba. Har wa yau rahoton ya ce irin wannan matan na daukar cikin ne ba tare da suna da muradin yin hakan ba sai dai kawai don basu da wani zabi da ya wuce hakan.

A wata zantawa da ya yi da manema labarai a birnin London na Birtaniya dangane da kunshin wannan rahoton, shugaban hukumar ta kula da yawan al'ummar ta Majalisar Dinkin Duniya Dr. Babatunde Osotimehin cewa ya yi "ummul aba'isin wannan matsala ba za ta rasa nasaba da rashin sanya yara mata a makaranta ba da tabarbarewar fannin kiwon lafiya da ma dai rashin aikin yi."

Tuni dai kungiyoyin fararen hula irin su Renate Baehr da ke wata gidauniya da ke sanya idanu kan yawan al'umma a duniya suka fara nuna rashin har ma suka ce barin wannan matsala na faru tauye hakkin yaran ne.

"Hujja ta dangane da wannan batu na tauye hakki ita ce yadda yara mata 'yan shekaru sha uku da haihuwa ke daukar ciki ba tare da son ransu ba. Hakan na gurgunta rayurwasu matuka."

Wannan yanayi da ake ciki ne dai ya sanya hukumar ta kula da yawan jama'a ta duniya ke ganin dole a tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen wannan matsala ta hanyar shimfida tsare-tsare da za su kai ga kawar da ita.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin