Kimanin mutane 31 sun hallaka a Philippines | Labarai | DW | 17.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kimanin mutane 31 sun hallaka a Philippines

Ana ci gaba da neman mutane masu yawa da suka bace bayan hadarin jiragen ruwa na Philippines

Akalla mutane 31 sun hallaka yayin da wasu daruruwa suka bace sakamakon taho mu gama tsakanin jirgin ruwan daukan fasinja da na dakon kaya, wanda ya faru kimanin kilo-mita 600 kudancin Manila babban birnin kasar Philippines.

Masu aikin gadin bakin teku na kasar sun yi nasarar ceto fiye da mutane 570, inda ake kyautata zaton mutanen da ke cikin jirgin ruwan fasinja sun kai 800, lokacin da hadarin ya faru, kusa da tashar jiragen ruwan Cebu, wanda ke zama birnin na biyu mafi girma a kasar. Lamarin ya faru lokacin da galibin fasinjoji ke barci.

Wasu rahotanni na cewa fiye mutane 200 suka bace, wadanda yanzu haka ake nema sakamakon faruwar hadarin na kasar ta Philippines.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh