Kiev ta kaddamar da yaki da ′yan aware | Labarai | DW | 13.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kiev ta kaddamar da yaki da 'yan aware

Ma'aikatar cikin gida ta kasar Ukraine ta sanar da kaddamar da shirin yaki da 'yan ta'adda domin kawo karshen tashin hankalin da gabashin kasar ke fama da shi.

Kamfanin dillancin labarai na Interfax ya ruwaito cewa ministan cikin gida na Ukraine din Arsen Avakov ne ya sanar da hakan inda ya ce tuni jami'an tsaro sun fara yaki da 'yan ta'addan a yankin Slavyansk. Rahotanni sun bayyana cewa 'yan aware da ke neman komawa karkashin ikon Rasha a gabashin Ukraine sun kwace iko da ofisoshi da hukumomin gwamnati masu yawa a yankin.

Tun dai bayan da aka kifar da gwamnatin tshohon shugaban kasar Viktor Yanukovych ake samun adawa da kuma tashin hankali a gabashin Ukraine da mafiya yawan mazaunansa suna amfani ne da harshen Rashanci kuma suna goyon bayan Rashan ne, wanda kuma kasashen yamma ke dora alhakin rikicin a kan Rasha, batun da mahukuntan na Moscow ke ci gaba da musantawa.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba