Khodorkovsky ya ce ba zai yi siyasa ba
December 22, 2013Talla
A karon farko tun bayan da aka sako shi daga gidan kurkuku a ranar Jumma'a da ta gabata, Khodorkovsky yayi wani taron manema labarai a birnin Berlin inda ya jadadda cewar zai yi hannun riga da al'amuran siyasa.
Ya ce :''Kokowar neman mulki ba tawa ba ce, haka na rubuta a cikin wasiƙar da na aike wa shugaba Putin.'' Khodorkovsky wanda ya kwashe kusan shekaru goma ana tsare da shi a gidan kurkuku a kan laifin da ake tuhumarsa da shi na cin hanci da zamba. Ya ce zai mayar da hankali ta yadda za a iya kawo ƙarshen samun fursuna na siyasa. Kuma ya miƙa godiyyarsa ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wacce ya ce ta taka rawa wajen ganin an sako shi.
Mawalafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman