Khalifa Haftar ya tsallake rijiya da baya | Labarai | DW | 04.06.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Khalifa Haftar ya tsallake rijiya da baya

Rahotanni daga Libya na cewar bijirarren janar din sojin kasar Khalifa Haftar ya tsallake rijiya da baya bayan da wani dan harin kunar bakin wake ya yi kokarin hallaka shi a yau.

Mai magana da yawun Mr. Haftar din Mohamed Hejazi wadan ya tabbatar da wannan labarin ya ce harin ya auku ne a wani gida da ke wajen birnin Benghazi inda wani dan harin kunar bakin wake cikin mota da ke makare da bama-bamai ya afka cikin gidan, lamarin da ya sanya mutane uku suka rasu.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kaiwa janar din hari tun bayan da ya ce ya daura damar yaki da abinda ya kira 'yan ta'adda a Benghazi a tsakiyar watan Mayun da ya gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu