1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kerry ya isa yankin Gabas ta Tsakiya

December 5, 2013

Batun nukiliyar Iran na shirin mamaye ziyarar aiki da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya fara a yankin Gabas ta Tsakiya da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa.

https://p.dw.com/p/1ATFP
Hoto: picture-alliance/dpa

Sakatare harkokin wajen Amirka John Kerry ya isa yankin Gabas ta tsakiya da nufin ci-gaba da lalubo hanyoyi samar da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Izra'ila da kuma Palasdinu. Ajendar babban jami'in diplomasiyar Amirkan ta tanadi ganawa da firamiistan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas.

Wani muhimmin batu da zai mamaye ganawa tsakanin Kerry da Netanyahu shi ne na tsaro bayan da aka cimma matsaya a kan nukiliyar Iran. Ita dai kasar Isra'ila ta danganta yarjejeniyar nukiliyar da "wani kuskure" saboda barazanar da ta fuskanta daga kasar Iran.

A karshen watan Yuli na wannan shekarar da muke ciki ne dai Kerry ya yi nasarar farfado da tattaunawar zaman lafiya da ta cije tun shekaru ukun da suka gabata tsakanin Isra'ila da kuma Palasdinu. Sai dai kuma tattaunawar na ci-gaba da tafiyar hawainiya duk da kai kawo da Kerry ya ke yi tsakanin bangarorin biyu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shahu Usman