Keita ya zama sabon shugaban Mali | Labarai | DW | 13.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Keita ya zama sabon shugaban Mali

Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zaben shugaban kasar Mali da aka gudanar zagaye na biyu.

A kasar Mali an zabi Ibrahim Boubakar Keita a matsayin sabon shugaban kasa, inda haka ya tabbatar tun kafin sanar da sakamakon a hukumance. Tuni abokin karawarsa Soumaila Cisse tsohon ministan kudi ya rungumi kaddara, sannan ya amince da sakamakon zaben tun cikin daren jiya Litinin.

Keita tsohon firaminista tun farko ana kyautata zaton dama zai lashe zaben wanda aka gudanar ranar Lahadi da ta gabata. Ya samu kashi 40 cikin 100 yayin zagayen farko na zaben da aka gudanar cikin watan Yuli.

Sabon Shugaban kasar na Mali, Boubakar Keita ya yi alkawarin dawo da mutuncin kasar a idon kasashen duniya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi cikin shekarar da ta gabata, abin da ya janyo 'yan aware suka mamaye yankin arewacin kasar, kafin fatattakar mayakan da kasar Faransa ta jagoranta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita Umaru Aliyu