Keita ya lashe zaben Mali da gagarumin rinjaye | Labarai | DW | 15.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Keita ya lashe zaben Mali da gagarumin rinjaye

Hukumomin zabe a kasar ta Mali sun ce Ibrahim Boubacar Keita ya samu kimanin kashi 78 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada a zagaye na biyu na zaben.

Sakamakon da aka bayar a hukumance a wannan Alhamis na zaben shugaban kasar Mali zagaye na biyu ya nuna cewa shugaban da aka zaba Ibrahim Boubacar Keita ya lashe zaben da gagarumin rinjaye. Hukumomin zabe a kasar ta Mali sun ce Keita ya samu fiye da kashi 77 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada yayin da abokin hamaiyarsa Souma'ila Cisse ya samu kimanin kashi 22 cikin 100. Sai dai yawan wadanda suka kada kuri'a a zaben na ranar Lahadi bai kai wadanda suka sauke wannan nauyi a zagayen farko na zaben ba. A hukumance kashi 46 cikin 100 na wadanda suka cancanci kada kuri'a a kasar suka sauke wannan nauyi. Ana sa rai a wata mai zuwa za a rantsar da Keita a mukamin shugaban kasa, watanni 18 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohuwar gwamnatin demokradiyyar kasar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu