1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kebbi: Matashiya mai abincin masu ciwon Suga

April 24, 2019

Wata matashiya Saratu a jihar Kebbi da ta kammala karatun ta na jami’a ta jingine kwalin digirin ta kuma rungumi sana’ar abinci mai gina jiki ga masu cutar ciwon Suga wato diabtes.

https://p.dw.com/p/3HLAL
Interwiew mit der Erfinderin des Kebbi Diät-Essens
Hoto: DW/M. A. Sadiq

Matashiyar Saratu Mohammad Sani ta ce wannan hanya ce ta bayar da gudunmuwa ga masu fama da ciwon Suga ta la’akari da cewa ba kowane irin abinci suke bukata ba.

Matashiyar ta bayyana dalilan da suka ja hankalinta ga wannan sana’a ta abincin masu ciwon suga.

Saratu ta ce sana’ar ta samu karbuwa matuka duk da cewa akwai kalubalen da ta fuskanta a yayin da ta fara sana’ar.

Yanzu haka dai Saratu na horar da dumbin matasa dubarun yin wannan girki na masu fama da cutar ciwon Suga dake zuwa daga wata cibiyar horar da matasa mai suna Sahihiyar rayuwa a Birnin Kebbi.

Al’umma da dama a jihar Kebbi sun yabawa wannan mataki na matashiyar na samar da abincin masu fama da ciwon Sugar.