Kazantar rikici a Sudan ta Kudu | Labarai | DW | 18.12.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kazantar rikici a Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 400 zuwa 500 ne suka rasa rayukansu a Sudan ta Kudu.

Wani Jami'in diplomasiyya na Majalisar ta Dinkin Duniya ne ya sanar da cewa mutane da dama sun rasa rayukansu a sabon rikicin da ya balle a kasar Sudan ta Kudu, biyo bayan wani yunkuri na juyin mulki da bai yi nasara ba, sai dai yace har yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba, duk kuwa da cewa asibitocin kasar na bada rahoton mutuwar mutane 400 zuwa 500.

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudun dai ta dora alhakin yunkurin juyin mulkin da aka yi mata a kan sojoji magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar da aka kora, inda kuma rahotanni ke cewa kawo yanzu gwamnatin ta kame mutane 10 da take zargi da hannu a ciki.

Kawo yanzu dai akalla mutane dubu 20 ne suka nemi mafaka a ofshin Majalisar Dinkin Duniya dake Juba babban birnin kasar, domin tsira da rayukansu.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh