1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kazamin fada a kasar Kongo

April 2, 2013

An yi wani artabu a Jamuhuriyar Demokradiyar Kongo tsakanin dakarun gwamnatin da mayakan kungiyar Mai-Mai a yankin Lubumbashi inda a kalla mutane 23 suka mutu wasu 54 suka samu raunuka

https://p.dw.com/p/187uT
Hoto: Reuters

 A wani rikicin da ya barke a 'yan kwanakin baya bayan nan a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo, rahotani sun tabbatar da kimanin mutane 23 ne dai suka kwanta damarsu tun bayan barkewar rikicin a makon nan da ya shige a yankin Lubumbashi inji kakakin gwamnatin kasar ta Kongo.

A kwanan baya ne dai aka yi wani artabu tsakanin dakarun gwamnatin da mayakan kungiyar Mai-Mai yayinda sama da mutane 54 suka samu raunuka ciki har da fararen hula kamar yadda sanarwar ta gwamnatin ta bayanar.

Rahotani sun ce mayakan sun kutso ne daga yankin katanga mai dimbin arzikin ma'adinai inda sukayi masayar wuta da dakarun gwamnatin da suka samu goyon bayan sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

Dama dai tun a shekara 1960 ne yankin na Katanga ya tada kayar baya na bukatar samun 'yancin gashin kansa a matsayin kasa mai cikakken iko.

Mawallafi: Issoufou Mamane

Edita: Issoufou Mamane