Kayan agajin Rasha sun maƙale a kan iyakar Ukraine | Labarai | DW | 13.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kayan agajin Rasha sun maƙale a kan iyakar Ukraine

Hukumomin Rasha sun miƙa wata takardar ta jerin abubuwan da kayan agajin suka ƙunsa, wanda suka aike zuwa gabashin Ukraine ga gwamnatin ƙasar da kuma Ƙungiyar Red Cross.

Wani kakakin Ƙungiyar ta Red Cross ya ce manyan motocin Rasha 280 waɗanda ke ɗauke da kayan agajin da suka haɗa da ruwan sha da abinci don taimaka wa jama'ar da yaƙi ya tagayyara a gabashin Ukraine sun isa a kan iyakar ƙasar, sai dai ya ce ba su tsallaka ba yazuwa yanzu.

Jerin gwanon motocin yana daf da kan iyaka da garin Kharkhiv wanda ke a ƙarƙashin iko dakarun gwamnatin na Ukraine. Tun farko fIraministan na Ukraine ya ce ba za su bari ba kayan agajin su shiga ba, saboda fargaban da suke da shi na yin amfani da damar Rashar ta shigar da makamai ga 'yan tawaye.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Suleiman Babayo