Kawo karshen zanga-zanga a Hong Kong | Siyasa | DW | 15.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kawo karshen zanga-zanga a Hong Kong

'Yan sanda sun afkawa wajen da masu zanga-zanga ta dimokradiyya a Hong Kong suka mamaye inda suka lalata tantuna da cire shingayen da suka killace wurin.

A wannan Litinin din nedai jami'an tsaro suka yi dirar mikiya a wuri na karshe da masu zanga-zangar suka mamaye tare da lalata shingaye da rumfunan da suka kakkafa.

Yayin wannan aiki na yau dai 'yansandan sun kame mutane da dama da kuma tarwatsa karin wasu sannan suka kawar duk wani abu da ke waje kana suka ayyana cewar an kawo karshen bore da aka kwashe makonni ana yi sai dai masu zanga-zanga far sun ce wannan ba zai sanyaya musu gwiwa ba kamar yadda wani matashi Ian Chan ke cewa.

Ya ce "ko da dai mamayar da muka yi ta zo karshe amma ina bada tabbacin cewa za mu cigaba da yin kokarin ganin an girka ingantaccen tsarin dimokradiyya a yanki kana mutanen Hong Kong su ma za su yi fafutukar ganin mulki na dimokradiyya ya samu."

Hongkong Protest Festnahmen 11.12.2014

Kame wasu masu gangamin

To sai dai yayin da Ian ke cewar suna nan daram kan bakansu, Leuk Tong na gani ba su kai ga samun biyan bukata amma fa za su sake damara don ganin sun sauya lamura a kasar.

"Ko kusa ba za mu ce mun yi nasara ba don kuwa muna nesa da ita to amma ba za a ce yunkuri ya fadi kasa banza ba domin kuwa ba mu mika wuya ba kuma ma wannan shi ne mataki na farko da muka dauka."

Ita ma dai Clara Tam cewa ta yi al'ummar yankin nan nan kan bakansu. Tashinsu da aka yi daga wuraren da suka killace ba ya na nufin kawo karshen fafutukarsu. Hasalima injita sun dau darasi kan ja da baya ba tsoro bane.

Ta ce "ni a ganina wannan fafutuka ba ta kare ba. Mutane da dama sun shige ta don neman ganin an samu tsarin dimokradiyya ingantacce. Da damarmu mun koyi darasi."

Hongkong Protest Camp wird aufgeräumt 15.12.2014

Kokarin share wuraren gangamin

Masu rajin kare hakkin bani adama daga sassa daban-daban na duniya dai yanzu haka na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu kan wannan yunkuri na gwamnatin Hong Kon inda da yawansu ke cewar hakan tamkar dukan mutum ne a hana hsi kuka, yayin da Ruby Chau da zaman mai fashin baki kan harkokin siyasa ke cewar matakin gwamnatin abin kunya ne wai rakumi ya shanye ruwan kaji.

"Wanan abu na da ban takaici. Gwamnatin Hong Kong ta bamu kunya kuma ba za mu taba sa ran samun abun kirki daga gare ta ba."

Abin jira a gani dai yanzu haka shi ne irin yadda lamura za su cigaba da kasancewa a Hong Kong musamman ma dai harkoki na kasuwanci da kuma irin mataki na gaba da masu zanga-zanga za su dauka kan wannan fafutuka tasu tun sun ce tarwatsa ba ya na nufin karya kashin bayansu ba ne.

Sauti da bidiyo akan labarin