Kawo karshen yakin a Kwalambiya | Labarai | DW | 24.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kawo karshen yakin a Kwalambiya

Gwamnatin Kwalambiya da kungiyar 'yan tawayen kasar ta FARC, sun sanya hannu a yarjejeniyar kawo karshen yakin mafi dadewa a Latin Amirka.

Wannan lamari dai ya dasa kyakkyawar fata a zukatan al'ummar kasar na ganin kasar na dab da samun kwanciyar hankali da zaman lafiya. Sanya hannu a kan yarjejeniyar ajiye makaman mayakan FARC dai ya tanadi shirin tattara mayaka a wuri guda har na tsawon watanni shida da fara aikin yarjejeniyar.

Shugaban Kwalambiya Juan Manuel Santos da jagoran 'yan tawayen Timoleon Jimenez suka ce suna fatan yarjejeniyar za ta kawo karshen yakin da kasar ke fama da shi sama shekaru 50.

Rahotanni na nuni da cewar, duk da farin cikin da al'ummar kasar ke ciki, akwai fargabar yiwuwar bullar wata kungiyar 'yan tawaye da za ta maye gurbin mayakan juyin juya halin na FARC.