1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Katar: Ana kada kuri'a a zaben 'yan majalisa

Abdoulaye Mamane Amadou
October 2, 2021

An soma zaben memebobin majalisar Shura ta Katar a karon farko tun bayan dage gudanar da zaben da ke zama zakaran gwajin dafi wa hukumomin kasar da ke shirin karbar gasar cin kofin duniya ta badi.

https://p.dw.com/p/41AVR
Symbolbild I Wahlen in Katar
Hoto: Mohamed Farag/AA/picture alliance

Kimanin 'yan majalisu 30 ne daga cikin memebobin majalisar 45 masu kada kuri'a ke zaba a wannan Asabar, a yayin da sarkin Katar Tamim bin Hamad Al-Thani ke da hurumin nada 15 daga cikinsu, kana kuma su kasance mafi karfin iko da karfin fada a ji a majalisar har ma su hau kujerar naki.

Kimanin 'yan takara 284 ne ke fafatawa a zaben, ciki har mata 28, wadanda ma'aikatar cikin gidan kasar ta sahalewa tsayawa takara bayan sun cika ka'ida, daga ciki har da Leena Nasser Al-Dafaa inda ta ce "Wannan shi ne mafrkina, babban burina shi ne na ganin mata sun samu matsayar da ta dace a cikin tafiyar da harkokin mulki, ta yadda za su bayar da tasu gunmawa. A lokacin da muke yara harkokin siyasa da na yau da kullun sun kasance karkashimn maza ne kawai, amma yanzu mun girma, kuma sarki ya fitar da mata daga duhu zuwa haske." Sai dai ka'idar zaben ta ce sai wadanda suka kasance 'yan kasar daga shekarar 1930 ne kawai, ka iya cancata a zabesu ko kuma su zaba, lamarin ya fitar da dama daga cikin masu kada kuri'a.