Katar ta hana Saudiya jigilar alhazanta
August 20, 2017Talla
Kasar Saudiya ta ce mahukuntan kasar Katar sun hana ta dauko maniyata bayan da Katar ta hana jiragen Saudiya sauka a filin jirgin saman kasar da ke Doha. Daraktan kamfanin sufurin jiragen sama na Saudiya Saleh al-Jasser ya ce ya zuwa wannan lokacin babu jirgin da ya dauko maniyyata kamar yadda aka shirya da mahukuntan kasar.
Wannan dai ba ya rasa nasaba da takaddamar da ke a tsakanin kasashen biyu bayan da Saudiya da wasu kasashen larabawa suka sanar da yanke hulda da kasar ta Katar bisa zargin ta da taimakawa ayyukan kungiyar IS