Kashe-kashe a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
May 16, 2014Talla
Mutane uku suka rasa rayukansu yayin da wasu biyar suka samu raunuka a wasu hare-harre da 'yan bindigan sa kai suka kai a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin arewa maso yammacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Waɗanda suka shaidar da lamarin sun bayyana cewar waɗanda suka aikatasu sun kwashi ganima, yayin da su kuma al'ummar garuruwan da ke kusa da garin Batangafo suka kaurace wa matsugunansu domin tsira da rayukansu.
Wani ɗan garin Batangafo inda waɗanda hare-haren ya shafa suka samu mafaka ya nuna takaicinsa dangane da aikata ta'asar da ake yi a gaban sojojin ƙasashen Afirka ta MISCA ba tare da sun ɗauki mataki a kai ba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdourahmane Hassane